Aƙalla mutum goma sha bakwai ne suka mutu yayin da wasu dubu sittin suka rabu da muhallansu sanadiyyar ambaliyar ruwa mafi muni ...
Aƙalla mutum goma sha bakwai ne suka mutu yayin da wasu dubu sittin suka rabu da muhallansu sanadiyyar ambaliyar ruwa mafi muni da aka gani cikin shekaru da dama a Malaysia.
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka kwashe kwana uku ana yi ya janyo mummunar ambaliya a jihohi takwas a Malaysia, inda ruwa ya cinye birane da ƙauyuka.
Wannan ya janyo fushi daga yan ƙasar kan hukumomin gwamnati inda suka zarge su da ƙin ɗaukar matakan gargaɗi ko kuma aika tallafi wajen kwashe mutanen da suka maƙale a wuraren da aka yi ambaliyar.
Akwai fargabar cewa za a samu ƙaruwar mutanen da suka mutu yayin da ake ci gaba da gano gawarwaki.
No comments