Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Yadda Turji Ke Tilasta Wa Zamfarawa Zuwa Abuja Nemo Kudin Biyan Haraji

Kasurgumin 'dan bindigar nan da ya addabi al’ummar Zamfara, Bello Turji ya tilasta wa magidanta yin balaguro zuwa babban bir...


Kasurgumin 'dan bindigar nan da ya addabi al’ummar Zamfara, Bello Turji ya tilasta wa magidanta yin balaguro zuwa babban birnin kasar Abuja domin tattaro masa kudaden harajin da ya yanke musu ko kuma ya aika su lahira kamar yadda RFI ta labarto.

Daya daga cikin magidantan da muka sakaya sunansa, ya shaida wa RFI Hausa cewa, Turji ya yanke wa kauyensu harajin Naira miliyan 17 da ya ce su  biya shi cikin mako guda zuwa makwanni biyu ko kuma su dandana kudarsu.

Tuni wannan bawan-Allah ya isa birnin Abuja, yana buga-bugan neman kason da aka yanke masa na Naira dubu 11 domin tsira da ransa da kuma na iyalansa kamar yadda ya shaida mana.

Kazalika mutumin ya bayyana cewa, Turji na yin zairga-zirgarsa tare da mukarrabansa cikin tinkaho tsakanin al’umma, inda har yake zuwa Masallacin Juma’a domin yin sallah ba tare da  wata farbaga ba.

‘Yan bindiga dai na ci gaba da kaddamar da hare-hare kan al’ummar yankin arewa maso yammacin Nijeriya musamman Zamfara da Sakkwato da suka fi fama da musibar ‘yan ta’addar.

‘Yan Nijeriya da dama na ci gaba da bayyana bacin ransu kan yadda gwamnatin kasar ta gaza tabuka abin kirki wajen shawo kan wannan matsalar tsaron baki-daya.

A baya-bayan nan, ‘yan bindigar sun kona wasu fasinjoji kurmus a cikin motarsu a jihar Sakkwato, lamarin da ya girgiza al’ummar Nijeriya, yayin da matasan kasar suka shirya gudanar da zanzga-zanga domin aika sako ga shugaban kasar Muhammadu Buhari.

No comments