'Yan Bindiga Sun Hallaka Kwamishinan Kimiyya Da Fasaha A Katsina


Wasu ƴan bindiga sun je har gida sun hallaka kwamishinan ma’aikatar kimiyya da fasaha na jihar Katsina Dr. Rabe Nasir.

Lamarin dai ya faru a cikin daren jiya inda suka dira gidansa da ke cikin rukunin gidajen Fatima Shema a cikin birnin Katsina suka kashe shi.

Bayanan da mu ke samu yanzu haka ana ƙoƙarin ɓalle ƙofar ɗakinsa domin a fito da gawarsa. 

Post a Comment

0 Comments