Gwamnatin Kaduna ta ce ‘yan bindiga sun kashe karin mutane 9 a wasu kananan hukumomin jihar guda hudu yayin wasu. hare-hare da s...
Gwamnatin Kaduna ta ce ‘yan bindiga sun kashe karin mutane 9 a wasu kananan hukumomin jihar guda hudu yayin wasu. hare-hare da suka kai a baya bayan nan.
Kwamishinan tsaron cikin gidan jihar ta Kaduna Samuel Aruwan ne ya bayyana haka, bayan samun rahotanni kan hare-haren daga rundunonin soji da ‘yan sanda, kamar yadda ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar a Juma’ar nan.
Aruwan ya ce kananan hukumomin da suka fuskanci hare-haren ‘yan bindigar sun hada da Chikun, Zaria, Igabi da kuma Zangon Kataf.
Kwamishinan ya ce a karamar hukumar Chikun an kashe mutane uku ne a yankin hanyar da ta tashi daga Kaduna zuwa Birnin Gwari, sai kuma wani mutu 1 a cikin garin na Chikun.
No comments