Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 38 A Jihar Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da kai kazamin harin da ya hallaka mutane akalla 38 a wasu kauyukan dake karamar hukumar Giwa...


Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da kai kazamin harin da ya hallaka mutane akalla 38 a wasu kauyukan dake karamar hukumar Giwa, yayin da aka konawa jama’a kayan abincinsu.

Kwamishinan tsaron Jihar Samuel Aruwan ya ce bayan kashe mutane an kuma kona gidaje da motoci manyan da kanana tare da amfanin gona a kauyukan Kauran Fawa da Marke da Riheya.

Aruwan ya ce tuni Gwamna Nasir El Rufai ya aike da sakon ta’aziya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su.

No comments