Daya daga cikin matafiyan da aka harba. Daga Wakilinmu Labarin dake shigowa MADOGARA na nuni da cewa wadansu 'yan bindiga ...
Daya daga cikin matafiyan da aka harba.
Daga Wakilinmu
Labarin dake shigowa MADOGARA na nuni da cewa wadansu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun farmaki matafiya a daidai garin Kucheri dake karamar Hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, inda suka kashe mutane hudu tare da garkuwa da mutum ashirin kamar yadda majiyarmu ta labarta mana.
Majiyarmu wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta labarta mana cewa harin an kai shi ne da misalin karfe 9 na daren jiya Juma'a 17 ga watan Disambar 2021.
Majiyar ta ci gaba da cewa; "Bayan 'yan bindigar sun jima da tare wannan hanyar, sai ga sojoji suka zo suka koresu. Bayan sun kore su ne, sai suma sojojin suka tafi, kwatsam sai ga su sun sake dawowa inda a nan ne suka kashe wasu mutane a mota tare da garkuwa da wasu".
"Sun kashe mutane 4 tare da garkuwa da akalla mutum 20", inji majiyar ta mu.
Garin Kucheri dai na kan titin Sakkwato ne, inda ba shi da wani tazara sosai da garin Yankara ta karamar Hukumar Faskari dake jihar Katsina da kuma cikin garin Tsafe ta jihar Zamfara.
No comments