’Yan bindiga sun kashe manoma biyu sannan suka sace wasu mutum 50 a kauyen Unguwar Gimbiya da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar...
’Yan bindiga sun kashe manoma biyu sannan suka sace wasu mutum 50 a kauyen Unguwar Gimbiya da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna kamar yadda Daily Trust ta labarto.
Shaidun gani da ido sun ce maharan dauke da muggan makamai sun kai farmakin ne a safiyar Juma’a inda suka shiga gidaje 13 suna barin wuta tare da cin karensu babu babbaka.
Wani dan Unguwar mai suna Gideon Jatau ya ce ba su taba ganin tashin hankali kamar wannan ba.
Ya ce, “Akan yi garkuwa da mutane jefi-jefi amma dai ba a taba yin mai muni irin wannan ba", inji shi.
A cewarsa, wasu mazauna Unguwar sun fara hijira saboda tsoron wani sabon harin.
Har zuwa lokacin kammala hada wannan rahoto dai babu cikakken bayani daga hukumomi game da harin.
No comments