Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da ‘Mutum 70’ A Hanyar Kaduna Zuwa Birnin Gwari

‘Yan bindiga a Nijeriya sun tare tawagar matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari inda suka kwashe mutane da dama suka gudu da su ci...


‘Yan bindiga a Nijeriya sun tare tawagar matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari inda suka kwashe mutane da dama suka gudu da su cikin daji.

Mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne da safiyar jiya Laraba a lokacin da matafiyan ke kan hanyar su ta zuwa Kaduna bayan sun bar Birnin Gwari.

Wani shugaban al’umma Muhammadu Umaru ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar daga cikin wadanda aka kwashe akwai makwabtansa guda 4 a cikin tawagar motoci 20 dake samun rakiyar jami’an ‘yan Sanda.

Umaru ya ce akalla matafiya 70 ke cikin tawagar daga garin Udawa, yayin da ya ce akwai kuma karin wasu mutane daga wasu garuruwa dake tsakanin Udawa da Buruku.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin wadanda suka gudu cikin daji sun kira ‘yan’uwan su inda suka shaida musu abin da ya faru.

Ya zuwa wannan lokaci, rundunar ‘yan Sandan Jihar Kaduna ba ta tabbatar da aukuwar lamarin ba tukuna.

 

 

No comments