Mazauna yankin gabashin jihar Sakkwato a Najeriya na ci gaba da bayar da rahotannin fuskantar hare-haren ‘yan fashin daji kan al’umomin da...
Mazauna yankin gabashin jihar Sakkwato a Najeriya na ci gaba da bayar da rahotannin fuskantar hare-haren ‘yan fashin daji kan al’umomin da ke yankin.
Duk da nasarorin da rundunar sojan kasar ta ce ta samu a cikin jerin hare-haren da suke kai wa a kwanannan kan mabuyar ‘yan fashin a yankin.
A cewar wadanda da BBC ta zanta da su, hare-haren sun fi kamari ne kan garuruwan da ke yankin karamar hukumar Sabon Birnin Gobir musamman daura da iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar.
Dan majalisa mai wakiltar yankin, Honarabul Abdullahi Muhammad Tsamaye, kuma tsohon shugaban karamar hukumar ne, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya munana.
Shi ma Sulaiman Isa, kansilan mazabar Makuwana ya ce hare-haren sun yi kamari sosai a mazabarsa tare da yin kira ga mahukunta da su baza jami’an tsaro zuwa dajin gundumi daga inda ya ce maharan suke fitowa.
Kokarin da BBC ta yi don jin ta bakin rundunar ‘yan sanda jihar kan wadannan rahotannin bai yi nasara ba.
Sai dai wannan na zuwa ne kwana da ya bayan da Hedikwatar tsaron kasar ta fitar wata sanarwa inda ta ce dakarun kasar sun kashe ‘yan fashin daji 33 tare da kama wasu da masu taimaka musu su 19.
Sun yi nasarar ne yayin hare-haren da suka kai yankin na gabashin Sakkwato da kuma yammacin jihar Zamfara mai makwabtaka a cikin makonni biyun da suka gabata.
No comments