Wasu 'yan daba sun kai hari filin da jam'iyyar PDP take gudanar da zabukan shugabanninta a Gusau, babban birnin jihar Zamfara. G...
Wasu 'yan daba sun kai hari filin da jam'iyyar PDP take gudanar da zabukan shugabanninta a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Gidan talbijin na Channels ya
rawaito cewa tun da fari an so a gudanar da taron a Zaitun Oil mill, da ke
bayan hukumar alhazai amma aka sauya zuwa Command Guest House da ke Gusau.
Rahotanni sun ce 'yan dabar siyasa
sun yi wa wurin dirar-mikiya da sanyin safiyar Litinin inda suka lalata kayan
zabe da fom-fom da motocin 'yan jam'iyyar PDP da kuma kujeru sannan suka cinna
wuta kan rumfunan da aka kafa.
Hotunan da aka rika watsa a shafukan
intanet sun nuna yadda wurin ya kama da wuta bayan an yi kaca-kaca da shi.
Rahotanni sun ambato Umar Aminu,
wani hadimin mataimakin gwamnan Zamfara, Mahdi Aliyu Gusau, yana cewa babu
wanda ya isa ya yi musu barazanar da za ta kai su fasa gudanar da taron.
An soma zaman doya-da-manja tsakanin
Gwamna Mohammed Matawalle da mataimakinsa tun bayan gwamnan, wanda aka zaba a
karkashin jam'iyyar PDP, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
No comments