Daga Umar Shuaibu Wata kungiya dake kunshe da jam'iyyun siyasa na 'yan Shi'a a kasar Iraki sun yi watsi da sakamakon...
Daga Umar Shuaibu
Wata kungiya dake kunshe da jam'iyyun siyasa na 'yan Shi'a a kasar Iraki sun yi watsi da sakamakon zaben kasar jim kadan bayan Hukumar zaben kasar ta sanar da sakamakon zaben. Kungiyar ta bayyana cewa ba za su taɓa amincewa da sakamakon zaben ba.
Kungiyar dake ikirarin samar da tsarin daidaito a kasar ta bayyana haka ne a wata sanarwar da ta fitar ranar talata 30/11/2021 da dare awanni kadan bayan sanar da sakamakon zaben 'yan majalisa da aka gudanar a kasar.
Sun bayyana cewa "Ba za su taɓa amincewa da sakamakon zaben ba; ko shakka babu, hukumar zaben ta shirya wannan sakamakon tun kafin gabatar da zaɓen".
"Saɓanin da aka samu tsakanin sanarwar hukumar zaben da bangaren Shari'a ya nuna cewa ba su dauki ƙorafin da mutane ke yi da muhimmanci ba".
Sanarwar ta kara da cewa, "Muna kyautata zaton cewa, kotun koli za ta duba ƙorafe-korafen al'umma da hujjoji masu karfi ta kuma dau matakin da ya dace ba tare da nuna ɓangaranci ba domin tabbatar da adalci tsakanin masu zaɓe da 'yan takara."
Yayin da shugaban hukumar zaben kasar yake bayyana sakamakon a jiya Talata ya tabbatar da cewa ƙorafe-korafen ya yi tasiri wurin sauya sakamakon zaben kujeru biyar ne kawai a yankunan Bagadaza, Ninawa, Erbil, Kirkuk da Basrah.
Sakamakon zaben ya nuna Ɓangaren Sadr ke da rinjaye da kujeru 73, sai kuma haɗin gwiwar 'yan sunna karkashin Muhammad Halbousi suka samu kujeru 37, sai kuma ɓangaren Nouri Al-maliki suka zo na uku da kujeru 33.
No comments