Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YANZU-YANZU: An Jiyo Karar Fashewar Wani Abu A Jihar Borno

Mazauna rukunin gidaje 1000 a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun farka da fashewar wani abu da safiyar yau Asabar. ...


Mazauna rukunin gidaje 1000 a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun farka da fashewar wani abu da safiyar yau Asabar.

Majiyar ta Jaridar Daily Trust ta labarto cewa; fashewar ana kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka yi shi, wanda hakan ya kawo rudani a tsakanin al’ummar yankin.

Wadansu bayanai har wala yau sun ce wani makamin roka ya sauka a filin jirgi na Gomari, yanki mai tazarar kilomita hudu daga filin jirgin da ke babban birnin jihar.

A cikin wani faifan bidiyo da Jaridar Daily Trust gani, ta kuma ruwaito, ta ce mazauna yankin na ta tofa albarkacin bakinsu. 

Ya zuwa hada rahoton nan, majiyarmu ta ce ba ta da tabbacin ko an samu asarar rayuka. 

Sai dai wata majiyar soji ta bayyana cewa, dakarun da ke dauke da Bataliyar ta 33, a Njimtelo, sun bude wuta ne a lokacin da suka hango 'yan ta'addan Boko Haram a wajen birnin Maiduguri.

An kuma ce maharan sun kuma yi artabu da sojoji yayin harin.

No comments