Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Za A Binciki Mai Horas Da Tawagar Kwallon Gabon Kan Zargin Lalata Da Yara

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo ya ba da umarnin gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa Patrick Assoumou Eyi, tsohon kocin ta...


Shugaban kasar Gabon Ali Bongo ya ba da umarnin gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa Patrick Assoumou Eyi, tsohon kocin tawagar kwallon kafa ta kasar ta ‘yan kasa da shekaru 17, dangane da yin lalata da matasan ‘yan wasan a lokacin da suke karkashin sa ta hanyar yi musu fyade.

Jaridar ‘The Guardian da ke kasar Birtaniya ce dai ta wallafa rahoton bankado zargin a ranar Alhamis da ta gabata.

Tuni dai hukumar kwallon kafa ta Gabon ta dakatar da Eyi daga bakin aiki.


Shugaba Ali Bongo, wanda ya bayyana lamarin a matsayin tashin hankali, ya baiwa ministan shari’a umarnin fadada binciken da za a gudanar kan cin zarafin kananan yara mata da maza ta hanyar fyade zuwa dukkanin nau’ikan wasanni a kasar, domin kawo karshen miyagun da suke lalata ‘ya’yan jama’a.

No comments