BBC ta labarto cewa a na ci gaba da shirye-shirye da za a shafe mako ɗaya ana yi a Afrika ta Kudu don nuna alhinin mutuwar Archbishop Desm...
BBC ta labarto cewa a na ci gaba da shirye-shirye da za a shafe mako ɗaya ana yi a Afrika ta Kudu don nuna alhinin mutuwar Archbishop Desmond Tutu.
Mai fafutukar kare haƙƙin bakaken fatar ya rasu da safiyar Asabar yana da shekaru 90.
Wakiliyar BBC ta ce da ma 'The Arch' kamar yadda ake masa laƙabi, ya shafe sama da shekara 20 yana fama da kansar marena.
Gwamnatin Afrika ta Kudu ta bayyana cewa za a yi jana'izar marigayi Tutu a ranar 1 ga watan Janairu.
Shugaba Cyril Ramaphosa ya ce za a yi ƙasa-ƙasa da tutar ƙasar don girmamawa ga marigayin.
Shugabanni a fadin duniya na ci gaba da ta'aziyyar mutuwar Mista Tutu, ciki har da Fafaroma Francis da Shugaba Biden na Amurka da Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya da ma Sarauniya Elizabeth ta Birtaniya.
No comments