Al'ummar Gambia na shirin kada kuri'a don zaben shugaban kasa a gobe Asabar, zaben da zai fayyace makomar tsohon shuga...
Al'ummar
Gambia na shirin kada kuri'a don zaben shugaban kasa a gobe Asabar, zaben da
zai fayyace makomar tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh wanda ke zaman gudun
hijira a wata kasa kamar yadda gidan Rediyon Faransa ya labarto.
Wasu
masharhanta na ganin cewa manyan batutuwan da za su yi tasiri wajen zaben ‘yan
takarar da za su fafata a zaben na Gambia baya ga sha’anin tattalin arziki, sun
hada da makomar tsohon shugaba Jammeh wanda ya mulki kasar tsawon shekaru 22
daga shekarar 1994, dangane da yiwuwar dawowarsa daga gudun hijira, da kuma
yadda zai mayar da martani ga laifukan da ake zarginsa da aikatawa a karkashin
mulkinsa wadanda suka hada da fyade, azabtarwa, da kuma kisan gilla.
An
tilasta wa Jammeh gudun hijira zuwa Equatorial Guinea ne a shekara ta 2017,
bayan da shugaba Adama Barrow, ya kayar da shi a zaben da suka fafata sakamakon
da fari tsohon shugaban ya so yin watsi da shi.
Sai
dai har yanzu Jammeh na da sauran goyon bayan siyasa a Gambia, inda masu
fafutukar kare shi suka matsa kaimi kan ya koma gida, yayin da kuma a gefe
guda, tsohon shugaban ya nemi yin tasiri a zaben na gobe Asabar da zai gudana,
inda ya yi jawabi ga gangamin magoya bayansa.
Lokaci
ne dai kawai zai fayyace makomar siyasar Gambia a zaben da ke zaman zakaran
gwajin dafin sabuwar dimokradiyyar kasar.
No comments