Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

ZAMAN LAFIYA: Garkuwan Matasan Arewa Ya Ja Hankalin Matasa

Daga Wakilinmu Alhaji Abdul-aziz Husaini garkuwan matasan Arewa kuma sarkin fadar Gini Moni ya shawarci matasan Arewa game da sa...


Daga Wakilinmu

Alhaji Abdul-aziz Husaini garkuwan matasan Arewa kuma sarkin fadar Gini Moni ya shawarci matasan Arewa game da samun tabbataccan zaman lafiya a kasa baki daya.

Garkuwan matasan ya shawarci matasan ne a lokacin da wakiliyarmu ta ziyarci fadarsa dake karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.

Alhaji Abdul-Aziz Husaini shi ne garkuwar matasan Arewa kuma Dan kasuwa mai jin tausayin talaka kuma Basarake mai son zaman lafiya a kodayaushe.

Don haka ne ya yi dubi ga abubuwan dake faruwa a halin yanzu a kasa baki daya kuma ya yi kira ga matasan Arewa baki daya.

Ya ce; "don Allah don Annabinsa duk wani matashi ya yi hakuri da rayuwa ya daure da halin da ake ciki a yanzu Allah zai kawo mana taimako".

Garkuwan matasan ya yi kira da cewa bai kamata matasa su zauna ba aikin yi ba wannan shi ke taimakawa wajen jefa matashi cikin wani yanayi mara kyau.

Don haka nema shugaban ya ce, wajibi ne  matashi ya daure ya nemi sana'a komin kankantarta idan ya daure Allah zai albarkaci sana'ar tasa a rayuwa.

Da shugaban ya juyo kan abubuwan dake faruwa yanzu tuni ya ja hankalin matasan da su guji shiga dukkan babin da ka iya kawo tashin hankali a kasa baki daya.

Kuma ya hori matasan da su zama wakilan samun zaman lafiya a duk Inda suke don samun nasarar ci gaban kasa baki daya.

Shugaban ya koka matuka akan matasa masu jawo fitina a tsakanin al'uma.

Don haka nema ya yi fatan duk inda matasa suke su guji daukar doka a hannunsu, ya ce, hakan ba tsari bane a kasa baki daya.

A zauna lafiya da juna shi ne kashin bayan arziki. Yace jama'ar Arewa da jama'ar kudu abokan zama ne tun asali don haka wajibi ne su yi hakuri da juna. Ya yi addu'ar neman zaman lafiya ga Nijeriya da duniya baki daya.

Ya yi wa shugaban kasa addu'ar Allah ya bashi dauriya da lafiya shugabancin kasa har zuwa wa'adinsa. 

No comments