Zan Tabbatar Da Sahihin Zaɓe A 2023 -Buhari


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba ƴan Nijeriya da sauran ƙasashen duniya tabbacin gudanar da sahihin zaɓe a 2023, tare da mika mulki cikin kwanciyar hankali.

A jawabin da ya yi a wajen wani taron da shugaban Amurka Joe Biden ya shirya, shugaba Buhari ya ce za a ƙarfafa hanyoyin da suka dace domin tabbatar da cewa an samu sauyin mulki cikin kwanciyar hankali da lumana, kamar yadda sanarwar da fadar shugaban ta fitar ta bayyana.

Sanarwar ta ce, Buhari ya shaida wa Biden cewa Nijeriya za ta ci gaba da goyon bayan mulkin ɗimokuradiyya a yammacin Afrika da Afrika baki ɗaya, kuma Nijeriya za ta ba ƙungiyoyin ECOWAS goyon baya wajen magance wannan ƙalubalen da kuma godiya ga goyon baya daga Tarayyar Afrika da Majalisar Ɗinkin Duniya.

Post a Comment

0 Comments