Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

2023: Tinubu Ya Bayyana Aniyar Tsayawa Takarar Kujerar Shugabancin Nijeriya

Jagoran jam’iyyar APC a Tarayyar Nijeriya kuma tsohon gwamnan jihar Legas Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya kawo karshen rade-raden ...


Jagoran jam’iyyar APC a Tarayyar Nijeriya kuma tsohon gwamnan jihar Legas Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya kawo karshen rade-raden da ake yi dangane da sha’awarsa ta tsayawa takarar neman kujerar shugabancin kasar.

Rfi ta ruwaito cewa Tinubu ya yi wa magoya bayansa bushara ne a yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja, bayan ganawa da shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.

Tinubu ya bayyana cewa ya shaidawa shugaban kasar aniyarsa ta shiga jerin masu neman maye gurbinsa idan wa’adinsa na biyu ya cika a shekarar 2023.

Koda yake an dade da ganin alamun tsohon gwamnan na Legas na fatan darewa kujerar shugabancin Najeriya, Tinubu ya dade yana kaucewa yin magana akan al’amarin, abinda ya haifar da muhawara a tsakanin ‘yan Najeriya akan hasashen da ake yi akan bukatar tasa da kuma irin salon mulkin da zai jagoranta, idan har burin na sa ya cika.

A watan Oktoban shekarar bara, Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya bi sahun sauran ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar wajen kaddamar da yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na Tinubu a 2023.

No comments