Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO ya ce yana da tabbacin za a kawo karshen annobar korona a shekarar 2022, amma har sai kasa...
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO ya ce yana da tabbacin za a kawo karshen annobar korona a shekarar 2022, amma har sai kasashen duniya sun yi aiki tare.
Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce yanzu duniya na da makaman yaki da kuma kare annobar Covid-19.
Yana gargadin cewa yadda duniya ke tafuyar da nau'in Omicron na bukatar a kara dagewa.
WHO tace tanason ganin an yi wa kashi 70 na adadin mutanen duniya nan da tsakiyar 2022, domin kawo karshen dokokin da ake kakabawa na wannan annoba.
Yanzu an cika shekara ta biyu tun bayan da aka samu bullar annobar korona garin Wuhan na China.
No comments