Daga Aisha Suleman Kaduna Aliyu yana daga cikin iyalin Alhaji Usman Abubakar da kuma Hajiya Amina Yusuf wanda aka haifa a ranar ...
Daga Aisha Suleman Kaduna
Aliyu yana daga cikin iyalin Alhaji Usman Abubakar da kuma Hajiya Amina Yusuf wanda aka haifa a ranar 26 ga watan Mayun shekarar 1988. Ya kammala makarantar Firamare dinsa a jihar Katsina ya kuma samu shaidar kammala karatun Sakandire dinsa daga makarantar Unity School Ringim da ke jihar Jigawa.
Ya ci gaba a Jami'ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto inda ya kammala digiri dinsa na farko a Biochemistry kafin ya tafi yi wa kasa hidima a jihar Abia.
Ya shiga aikin dan sanda a ranar 9/1/2021 kuma ya samu shaidar manyan digiri har guda uku yana cikin aiki, 2 a Nijeriya 1 a kasar Jamhuriyar Ireland a karkashin tallafin karatu na ofishin jakadancin kasar Ireland.
A cikin shekarar 2017, Aliyu ya kasance dan Nijeriya na farko da aka bai wa lambar girmamawa ta Mandela Washington Fellowship for Young African Leaders inda a nan ya karanta Public Management ne a Jami'ar Syracuse University da ke New York. A cikin shekarar har ila yau ya zama na farko da ya karbi lambar yabo ta Roger Casement Fellowship in Human Rights kuma ya zama dan Nijeriya na farko da ya karbi lambar yabo ta Irish Aid Fellowship.
Ya yi kwasa-kwasai da dama a cikin Nijeriya da kuma a wasu kasashen.
Ya taba zamowa jami'i hulda da jama'a na shiyyar 'yan sandan jihar Kaduna.
Kafin nada shi jami'i mai kula da bayanai na sirri na Gwamnan jihar Zamfara, yana aiki ne a shiyyar kula da ayyuka a cibiyar hukumar 'yan sandan Nijeriya da ke Abuja.
No comments