Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

AFCON: Yadda Nijeriya Ta Lallasa Masar Da Kwallo 1 Mai Ban Haushi

Kelechi Iheanacho na Super Eagles ya cirewa Najeriya kitse a wuta a karawarta da Masar a jiya talata bayan kwallonsa da ta bai w...


Kelechi Iheanacho na Super Eagles ya cirewa Najeriya kitse a wuta a karawarta da Masar a jiya talata bayan kwallonsa da ta bai wa kasar ta yammacin Afrika nasara a wasanta na farko karkashin gasar cin kofin Afrika. 

Iheanacho da ke taka leda da Leicester City mai doka firimiyar Ingila ya shiga gaban takwarorinsa ‘yan wasan Firimiya wato Mohamed Salah na Liverpool da Riyad Mahrez na Manchester City da suka gaza zura kwallo a gasar wadda suke wakiltar kasashensu, ko da ya Iheanacho ya bi sahun Sadio Mane da shima ya fitar da kasarsa kunya a jiya.

A minti na 30 da fara wasa ne tauraron na Leicester ya zurawa Super Eagles kwallonta wanda ya bai wa Najeriya damar zama jagorar rukuninta na D da maki 3.

Yayin wasan dai Salah kaftin din tawagar ta Masar ya fusata matuka bayan mai tsaron ragar Najeriya ya barar da kwallon da ya yi kokarin zurawa a mintuna gab da karkare wasa bayan komawa daga hutun rabin lokaci.

Iheanacho dai ya lashe kyautar gwarzon dan wasa na karawar ta Najeriya da Masar.

A haduwa 8 da Najeriya ta yi da Masar a tarihi, sau 4 Super Eagles na nasara kan Pharaohs yayinda ta yi canjaras sau biyu ita kuma ta yi nasara a wasa biyu.

No comments