Daga Hauwa'u Abubakar Cibiyan nan mai binike akan ci gaban kasa da Dimokuradiyya da ake kira CEDDERT wato 'Center For De...
Daga Hauwa'u Abubakar
Cibiyan nan mai binike akan ci gaban kasa da Dimokuradiyya da ake kira CEDDERT wato 'Center For Democratic Development Research and Training', ta dukufa wajen bayar da tabbataccen rahoto akan bambancin dake tsakanin Almajiranci da kuma Bara a fadin kasarmu Nijeriya baki daya.
Cibiyar dai ta shahara wajen gudanar da bincike a bangarori da dama musamman a bangaren ilimi da tsaro da harkokin yau da kullum.
Wannan cibiya ta zama gagara misali akan gudanar da bincike a kowanni bangare a gida Nijeriya da da kasashen ketare.
Tuni cibiyar ta mallaki rijistanta a gida da waje domin taimakawa al'ummar Nijeriya.
Marigayi Dakta MD Yusuf na jihar Katsina da Marigayi Dakta Bala Usman suka kafa wannan cibiyar tun 1992 ba don komai ba sai domin kawowa wannan kasa ci gaba ta kowanne fanni musamman a bangaren Dimokuradiyya.
A yanzun kuwa wasu bayin Allah ne da suka tsotsi ilimin daga gare su suke jan ragamar wannan cibiyar domin taimakon kasa da kasa.
Farfesa Muhammad Mustafa Gwadabe da Farfesa Abdulkadir Adamu da dai sauran hazikan Malamai suke jan ragamar cibiyar a halin yanzu.
Wakiliyarmu ta ziyarci wannan cibiya domin jin ko ina tasa gaba akan bincike da suke gudanarwa a bangarori da dama?
Cikin binciken da suke a yanzu akwai binciken akan hana almajiranci a wannan kasa wanda a ganin masanan hakan akwai gyara tunda ba wani bincike aka yi ba akan wannan mataki da aka dauka.
A bisa haka ne Farfesa Gwadabe ya yi karin bayani akan lamarin a yayin zantawarsu da manema labarai a Sakateriyarsu dake Zangon Shanu Zariya a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.
Farfesa Gwadabe bayan ya kawo tarihin wannan cibiya kuma ya jinjinawa wanda suka kafa wannan cibiya da kuma wanda suke bayar da gudummawarsu a halin yanzu kuma ya ce tuni suka fara bitar da wasu binciken da suka gabatar akan abubuwa da dama da suka addabi wannan kasa kuma ya koka akan ko in kula da ake yi da binciken da suke mikawa hukumomi domin daukar mataki. Farfesan ya bayar da misali da lokacin COVID 19 ta shigo da wasu suka tsaya dole sai an kawar da harkar almajiranci a kasa baki daya.
"Mu a namu hankalin sai muka ga cewa kamata ya yi tunda ana Dimokuradiyya ne, to bincike ya kamata a yi kafin zartar da hukunci", inji shi.
Ya ce a bisa haka ne yasa muka ce ya kamata a fahimci shin almajirancin tukunna wato ya kamata a sani almajiranci bara ne? Ko ko almajiranci hanya ce ta neman ilmin addini?", Ya tambaya.
"Wannan yanayi ne ya kai mu ga wani binciken tare da samun gudummawa daga 'MacArthur Foundation' wacce ta bamu wancan gudummawar a baya da muka gudanar da bincike akan ilmi kuma ta yaba kwarai da kokarinmu", ya tabbatar.
"Bisa haka ne ma suka ce mana me yasa ba za mu yi bincike akan Harkar almajiranci ba domin a sami madafa guda daya a kasa baki daya? Bisa yadda lamarin yake cikin tarihi me yasa ake samun matsala a yanzu? Suka ce yakamata a sami matsaya a kansa. Akan haka muke gudanar da binciken a halin yanzu. Domin akwai bambanci tsakanin bara da almajiranci", ya jaddada.
Ya ci gaba da cewa; "Domin yawancin yaran da ake gani da kwano da yawa su ba yaran da suke almajiranci bane, amma akwai yaran da suke almajiranci. Wasu daga cikin yaran daga gidan iyayensu suke fitowa da kwano suna bara a matsayin almajirci. Wannan ne ya nuna mana cewa jama'a na cikin wahala. Da yawa iyaye sun gaza rike yaransu wajen ba su abinci da tarbiyya saboda halin da suke ciki na karacin abin amfani na yau da kullum", inji shi.
Ya kara da cewa; "Mun zanta da Alarammomi akan haka sai muka gano cewa wasu yaran da ake kawo wa da yawa daga cikinsu sun fi karfin iyayensu ne. Bincikenmu ya nuna mana cewa duk abin da kake so ka ko yawa wani to ka koya masa tun yana yaro kamar abin da ya shafi yare. Harkar karatun Allo ta zama dole a raya ta bai kamata a ce an hanata ba", ya jaddada.
Ya nusasshe da hanyoyin da suke bayar da shawara, inda yake cewa; "Hanyoyin da muke bayar da shawara a bi sune; yakamata mutane su dauki nauyin lamarin. Hanyar da za a bi shi ne musulmi suke yinsa to Musulunci ya ce a bayar da zakka. Bayan haka gwamnati sai ta kafa kwamiti mai karfi a kasashen Musulunci kuma kwamitin a sanya shi karkashin mutane amintattu. Daga nan sai a yi tsarin da mutane za su rinka bayar da zakkar", ya lurantar.
"Bayan haka idan an karbi zakkar akwai wanda yakamata a ba zakkar ciki har da almajirai. To me yasa ba za a tsara karbar ba tare da rabawar ba?", Ya tambaya.
Ya kara da cewa: "Yakamata a samu wanda zai tsara duk inda almajirai suke domin hakan zai sa jama'a su fi amince da su. Kuma bai dace a ce an sami makarantu kusan 10 a Anguwa daya ba. Kuma suna abu iri daya maimakon hakan a hada su waje guda mana. Abin nufi ba mu ce ka gina masu gidan sama ba, a'a a sama masu makewayi da dan inda za su kwanta hakazalika in an tara zakkar a sami tsarin da zai rika samun abin da za su dan rike kansu.
"Duk wanda ka yi wa haka a shekara 4 da ikon Allah an rage masa nauyi mai yawa a rayuwarsa kuma sai ya komawa ga iyayensa don samun wani sana'ar da zai ci gaba da rayuwa. Muna da tabbacin in aka yi wa almajiranci kyakkyawan tsari za a magance matsalar da ake kakaba ma tsarin. Tabbas wata damuwar ana kakaba ta ne kawai saboda kiyayya.
"Misali an ce wai almajirai ne ke haddasa tashin hankali amma ba ka taba kama wani almajiri da laifin tashin hankali ba. Dalilin ko don ana ganinsu kawai a gari shiyasa ake jifansu da kalmar tashin hankali. Abin ban takaici duk masu yarfen ba za su iya bambance maka almajirai da almajiranci ba. Don haka wannan cibiya ta yi nisa akan wannan bincike kuma ta zanta da bangarori da dama ciki harda Malamai da almajirai da mutanen gari", inji Farfesa Gwadabe.
"Yanzun haka muna da murya da hoto mai motsi da mara motsi domin tabbatar da bincike mai inganci", ya lurantar.
Da yake amsa tambayar kalubalen da ita wannan cibiya ke fusakata, Farfesan ya ce tabbas akwai kalubale mai yawa; "Na farko wanda kake yi dominsu ba sa fahimtarka to amma me ya kawo haka? Tun farko gwamnati ta muna ba ta yi da su, sannan akwai wahalhahu da dama domin akwai lokacin da muka je Birnin Gwari to wahalar rashin kyan hanya kawai shima wani abun takaici ne da kalubale ga shi aikin binciken. Ga matsala ta rashin yarda da za a rinka nuna maka. Ga rashin tsaro don ma lokacin da muka je yankin akwai jami'an soja a yanki to mun sami dan sauki", ya labarta.
Ya kara da cewa; "wani misali akwai wadanda muka so mu yiwa tambayoyi a wani kauye, to wallahi tsoro ya hana ka da mu yi a biyo su daga baya a samu matsala. To amma dole a yi wannan aikin dole wasu su sadaukar da rayuwarsu don su ceto al'umma kuma mu akan haka muke Hatta tsakaninmu da gwamnatin akwai kalubale mai yawa don za ka ga ka yi bincike akan lamarin da zai amfanar da kasa amma an mashi rikon sakainar kashi ba a dauke shi. Ba a ba bincike muhimmanci a halin yanzu ka ha ai hakan ai kalubale ne babba", ya nusasshe.
A ƙarshe Farfesa ya shawarci gwamnati da al'umma su duba wannan lamari don daukar mataki.
No comments