Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Akwai Dangantaka Tsakanin Malamai Da 'Yan Jarida, Cewar Shugaban F.C.E Zariya

Tawagar 'yan Jaridar a yayin ziyarar da suka kai masa.  Daga Aisha Ibrahim Zariya Wannan jawabin ya fito ne daga bakin shugaban ...

Tawagar 'yan Jaridar a yayin ziyarar da suka kai masa. 


Daga Aisha Ibrahim Zariya

Wannan jawabin ya fito ne daga bakin shugaban Kwalejin Ilmi na Tarayya dake Zariya wato F.C.E.Zaria a yayin da shugaban ke karbar ziyarar fatan alheri bisa tabbatar da shi a matsayin shugaban Kwalejin daga wajen kungiyar 'Yan Jarida ta kasa reshen Zariya wato NUJ Zariya Unit a karkashin jagorancin shugaban kungiyar ta shiyyar Malam Sagir Awwal Abubakar.

A jawabin shugaban Kwalejin ya tabbatar da cewa 'yan jarida na daga cikin wadanda suka bayar da gudummawarsu wajen tsayuwarsa a wannan kujera ta hanyar yada abubawan alheri da suke yi wa makarantar bakin gwargwadon, a don haka ya ce "ina matukar godiya".

Dakta Balarabe ya cewa tawagar kofa a bude take a duk lokacin da kungiyar take bukatar wani taimako domin kawo ci gaban kasa.

Shugaban Kwalejin ya kara da cewa yana fatan kungiyar za du ci gaba da yada labaran da za su kara kawo zaman lafiya a tsakanin juna musamman yadda aikin jarida yake da kamanceceniya da aikin koyarwa a bangaren harkar ilimantarwa na kasa baki daya.

A karshe Dakta Balarabe ya ce Allah yasa masa sha'awar aikin jaridar tun farkon rayuwarsa a don haka ya ce, duk inda yake yana girmama 'yan jarida bisa haka ne yayi kira ga tawagar 'yan jaridar da su rike gaskiya da rikon amana a bakin aikinsu na fadakarwa da ilimantarwa a fadin kasa baki daya.

Da yake maida bayani shugaban tawagar ta manema labaran Malam Sagir ya ce, "A gaskiya mun ji dadin yadda aka karbe mu kuma da ikon Allah za a hadu a yi aiki tare don kawo ci gaban kasa". 

A karshe Malam Sagir da tawagarsa sun yi fatan alheri ga shugaban.

No comments