Allah ya yiwa fitaccen Malamin addininin Musuluncin nan, Dr Ahmad Muhammad Bamba rasuwa.
Daya daga cikin 'ya'yansa, Ahmad Muhammad Ahmad ya tabbatar da rasuwarsa a shafinsa na Facebook, inda ya rubuta cewa; "Allah ya yi wa babana Dr. Ahmad Muhammad Bamba rasuwa. Za a yi masa sallah bayan sallar Jumma'a a masallacin Darul Hadith".
0 Comments