Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

An Ɗage Haramcin Amfani Da Babura Masu Ƙafa Biyu A Arewaci Da Yammacin Yobe

Gwamnatin jihar Yobe ta sanar da ɗage haramcin amfani da babura masu ƙafa biyu a arewaci da yammacin Yobe. Wata sanarwa mai ɗauk...


Gwamnatin jihar Yobe ta sanar da ɗage haramcin amfani da babura masu ƙafa biyu a arewaci da yammacin Yobe.

Wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai ba wa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro Janar Ɗahiru Abdussalam, ta ce ƙananan hukumomin da aka ɗage haramcin sun haɗar da Fika, da Fune, da Nangere, da Potiskum, da Bade, da Machina, da Nguru, da Jakusko, da Karasuwa da kuma Yusufari.

Sai dai duk da wannan mataki gwamnatin jihar ta sanya wasu sharuɗa ga masu amfani da baburan da suka haɗar da amfani da su kawai daga ƙarfe 6 na safe zuwa 6 na yamma, sannan ban da goyo.

An kuma ba su umarnin yin rijistar baburan na su kana za su yi zirga-zirga ne a iya ƙananan hukumomin da suke ban da tsallakawa wata ƙaramar hukumar.

No comments