Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

An Bai Wa Gwamnatin Buhari Shawarar Kara Farashin Fetur Zuwa Naira 302

  BBC ta labarto cewa watakila gwamnatin Najeriya ta kara farashin man fetur zuwa naira 302 a kan kowa ce lita a wata mai zuwa, Fabrairu, ka...

 


BBC ta labarto cewa watakila gwamnatin Najeriya ta kara farashin man fetur zuwa naira 302 a kan kowa ce lita a wata mai zuwa, Fabrairu, kamar yadda majalisar kasa kan tattalin arziki ta bayar da shawara a watan Nuwamba na 2021, kamar yadda jaridar TheCable ta labarto.

Jaridar ta ruwaito cewa tana ganin wannan na daga cikin shirin gwamnati na janye hannunta kacokan daga harkar sanya farashin man, domin kawo karshen tallafin da take biya a kowane wata, ta yadda kasuwa za ta yi halinta a samu gogayya kan farashin.

A yanzu dai ana sayar da man fetur a yawancin sassan Najeriya a tsakanin naira 162 da 165 a kan kowace lita.

Kwamitin wucin-gadi na majalisar kula da tattalin arziki wanda ya tattauna da kamfanin mai na kasar (NNPC) a kan farashin da ya dace a sa shi ne ya bayar da shawarar kara kudin ta hanyar janye tallafin.

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai, wanda shi ne shugaban kwamitin, shi ya gabatar da rahoton.

No comments