Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Binne Mutum 143 Da Ƴan Bindiga Suka Kashe A Zamfara

BBC ta labarto cewa; aƙalla gawarwakin mutum 143 aka gano kuma aka binne bayan wani hari da ƴan bindiga suka kai a ranakun Larab...


BBC ta labarto cewa; aƙalla gawarwakin mutum 143 aka gano kuma aka binne bayan wani hari da ƴan bindiga suka kai a ranakun Laraba zuwa Alhamis a ƙauyuka da dama da ke ƙarƙashin Ƙananan Hukumomin Anka da Bukuyyum da ke Jihar Zamfara.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa ko a jiya Juma'a, sai da aka gano gawarwaki daga wasu dazuka.

Haka kuma rahotanni na cewa akwai gawarwakin wasu da ƴan bindigan suka kashe da aka daddatsa wasu kuma aka ƙona wasu ƙurmus.

Wani mazaunin yankin da lamarin ya faru ya shaida cewa akwai wani lamari mai ban tsoro da ya faru inda yan bindiga suka cinna wa gidaje wuta, gidajen akwai mata da yara a ciki kuma suka hana su fitowa haka suka ƙone ƙurmus.

Rahotanni sun ce rundunar sojin Najeriya ta tura jirgin yaƙi domin fatattakar ƴan bindigan amma jirgin ya kasa yin komai sakamakon ƴan bindigar sun shiga sun saje da al'ummar gari wanda abu ne mai wuya ga jirgin ya gano ƴan bindigar.

A ƴan kwanakin nan dai ƴan bindigan suna gudun hijira zuwa yammacin Zamfara inda suke guduwa daga farmakin da sojoji suke kai musu da kuma jirgin yaƙi.

Ƙauyuka da garuruwa da dama a Jihar Zamfara na fuskantar barazana da hare-hare daga ƴan bindiga. Gwamnati ta bayyana cewa an tura dubban jami'an tsaro domin yaƙar waɗannan ƴan bindigan.

No comments