An binne Bashir Tofa a kusa da mahaifinsa Zanna Alhaji Othman Tofa da mahaifiyarsa Hajiya Ruqayya (Inna) a maƙabartar da ke kan Titin Kats...
An binne Bashir Tofa a kusa da mahaifinsa Zanna Alhaji Othman Tofa da mahaifiyarsa Hajiya Ruqayya (Inna) a maƙabartar da ke kan Titin Katsina.
An yi jana'izarsa ne a birnin Kano bayan ya rasu ranar Litinin a Asibitin Malam Aminu Kano yana da shekara 74.
Wasu makusantansa sun tabbatar da cewa tsohon dan siyasar ya yi fama da jinya.
Shi ne tsohon ɗan takarar shugabancin Nijeriya a zaɓen shekarar 1993 ƙarƙashin jam'iyyar National Republican Convention (NRC).
A makon jiya ne aka yi ta watsa labarin da ke cewa Bashir Tofa ya rasu, amma daga bisani aka tabbatar bai rasu ba.
No comments