Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Kai Wa Gidan Dan Sanda Mai Yaki Da ’Yan Ta’adda Hari A Zariya

Aisha Suleman, Zariya Mahara dauke da muggan makamai sun kai hari gidan ASP Aliyu Umar, daya daga cikin jami’an ’yan sanda da ke...


Aisha Suleman, Zariya

Mahara dauke da muggan makamai sun kai hari gidan ASP Aliyu Umar, daya daga cikin jami’an ’yan sanda da ke aikin yaki da ’yan bindiga a Zariya ta jihar Kaduna.

Maharan da suka kai harin tun da misalin karfe 9:00 na dare, an yi ta artabu da su har kusan karfe 12:00 na daren Litinin, kafin daga bisani jami’an tsaro su kawo dauki.

Majiyarmu ta tabbatar da cewa maharan, sun fito ne ta dajin da ke hanyar makarantar ’yan mata ta Kofar Gayan a Kafa, dauke da muggan makamai sannan suka kuma yi wa gidan jami’in kawanya inda sukayi ta harbe-harben kan mai uwa da wabi.

Gidan ASP Aliyu dai na dauke da mutane sama da 20, ko da yake maharan ba su samu nasarar shigarsa ba.

Sai dai akwai yakinin sun hallaka wasu mutum biyu wadanda ake tsammanin masu kiwon shanu ne a wajen Kofar Kona da ke Zariya, kamar yadda wata majiyarmu ta tabbatar.

Majiyar tamu ta ce harin shiryayye ne musamman don a halaka jami’in tsaron da ake ganin yana namijin kokari wajen yaki da ’yan bindigar.

Ta kuma ce jami’an tsaro na ’yan sanda da soja da ’yan sa-kai sun taka muhimmiyar rawa wajen dakile harin, inda bayan sun kori maharan, suka samu nasarar kwato shanu masu yawan gaske da maharan suka kwashe na makiyayan da ke zaune a kusa da wajen.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai ba a sami tabbacin yawan mutanen da suka rasa rayuwankansu ba da kuma wadanda aka yi awon gaba da su ba.

Yanzu haka dai jama'a sun dukufa da addu'ar neman tsari daga sharrin maharan a gidaje da masallatai.

Bangaren jami'an tsaro ko sun kara jan damara don kare ruyuka da dukiyar jama'a a Zariya da kewaye.

No comments