Kusan ƴan Nijeriya 50,000 ne suka sanya hannu a kan wani ƙorafi da ke kira kan a soke jarrabawar gwajin iya Turanci don neman gu...
Kusan ƴan Nijeriya 50,000 ne suka sanya hannu a kan wani ƙorafi da ke kira kan a soke jarrabawar gwajin iya Turanci don neman gurbin ƙaro karatu a ƙasashen waje wadda ake kira IELTS.
Mafi yawan mutane a ƙasar na ganin wannan jarrabawa a matsayin rashin adalci.
Mafi yawan waɗanda suka sanya hannu kan ƙorafin waɗanda matasa ne, suna tattaunawa kan IELTS, wadda an tsara ta ne don ƴan ƙasashen da ba a Turanci a can, kuma Cibiyar Yaɗa Al'adu ta Birtaniya British Council ce, ke tsara ta.
Masu ƙorafin sun kafa hujja da cewa tun da Turanci shi ne yaren da ake amfani da shi a hukumance a Nijeriya - to ya kamata a cire ƙasar daga yin jarrabawar.
Jarrabawar wadda ake biyan dala 200, wato naira 100,000 har da ɗoriya, dole ce yin ta ga duk wanda yake son yin karatu a Birtaniya da Turai da kuma Amurka, kuma amfaninta kan ƙare ne bayan shekara biyu da yin ta.
Mutane da dama na mamakin dalilin da zai sa a ce amfaninta zai ƙare bayan shekara biyu.
No comments