An rantsar da Adama Barrow a matsayin shugaban Gambia a wa'adi na biyu bayan Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar da ya samu. F...
An rantsar da Adama Barrow a matsayin shugaban Gambia a wa'adi na biyu bayan Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar da ya samu.
Fadar shugaban ƙasa ta wallafa bidiyon shugaban mai shekara 56 yana shan rantsuwar kama aiki.
Jam'iyyar adawa ta United Democratic Party (UDP) ta ƙalubalanci sakamakon zaɓen na watan Disamba da Mista Barrow ya lashe da kashi 53 cikin 100.
UDP ta ce zaɓen na cike da abubuwan da ba su kamata ba. A ranar Litinin ne kuma kotun ta jaddada hukuncinta na yin watsi da ƙarar.
Barrow ya doke shugaban ƙasa mai-ci, Yahya Jammeh, a zaɓen 2017. Sai dai kuma shugaban ya ƙi yarda ya sauka daga mulki, abin da ya jawo tsaiko kafin Barrow ya shiga ofis.
No comments