Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Asarar Rayuka: Gwamnan Jihar Borno Ya Kaiwa Al'ummar Jihar Zamfara Ziyarar Jaje, Ya Bada Tallafin Miliyan 20

Daga Hussaini Ibrahim, Gusau A yau Litinin Gwamnan jihar Borno Farfesa Baba Gana Zulum ya kai ziyarar jajantawa ga al'ummar ...Daga Hussaini Ibrahim, Gusau

A yau Litinin Gwamnan jihar Borno Farfesa Baba Gana Zulum ya kai ziyarar jajantawa ga al'ummar jihar Zamfara sakamakon kisan Kiyashi da 'yan bindiga su kai wa al'ummar kananan hukumomin Anka da Bukuyum.

Gwamnan Zulum ya bayyana rashin jindadisa akan yadda 'yan bindigar su ke kisan al'umma ba tare da wani dalili ba kuma babu dare babu rana inji gwamna Zulum.

A jawabin nasa a gidan gwamnati, gwamna Zulum ya bayyana cewa, jihar Zamfara da Borno Danjuma ne da Danjummai wajen matsalar tsaro.

"Sakamakon matsalar tsaro a jihar Borno an yi asarar rayuka da dama kuma wadannan 'yan ta'addan sun yi ta'addancin wanda hankali ba ya dauka don sun tarwatsa makarantu, asibitoci, madatsun ruwa duk abin da dan Adam ke amfana da shi wajen tafiyar da rayuwar mu 'yan ta'addan sun wargaza", inji gwamna Zulum.

Gwamnan Zulum ya yi kira ga al'ummar jihar Zamfara da su dukufa wajen yin tuba ga Allah akan laifukan da suke aikatawa da kuma tawassuli da ayyuka na gari dan Allah ya kawo mana dauki akan matsalar tsaron. Kuma a nan take gwamna Zulum ya bada tallafin naira miliyan ashirin ga wadanda wannan masifa ta rutsa da su. 

A nasa jawabin gwamna Bello Matawalle ya bayyana godiyarsa ga gwamna Zulum akan tattakin da ya yi na ziyarar jaje gare su; "Allah ya saka da alhairi amin".

Gwamna Matawalle ya bayyanawa tawagar jajen irin asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi da kuma kokarin da gwamnati ke yi na ganin ta kawo karshen wannan ta'addancin. 

No comments