Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

AURE YA ƊAURU! Editan MADOGARA Ya Angwance

Alhamdulillah! Allah ya ƙaddari an ɗaura auren Ɗan Jarida, kuma Babban Editan MADOGARA, Mallam Ammar Muhammad Rajab, tare da Ama...


Alhamdulillah! Allah ya ƙaddari an ɗaura auren Ɗan Jarida, kuma Babban Editan MADOGARA, Mallam Ammar Muhammad Rajab, tare da Amaryarsa Malama Maimunatu Naseer Aliyu Na'Allah Zurmi.


An ɗaura auren ne a jiya Juma'a 21/01/2022 da misalin ƙarfe 1:30na rana a babban masallacin Juma'a na Sheikh Lawal Abubakar da ke Gada Biyu cikin babban birnin Gusau, Jihar Zamfara.

                 Shaidar daurin auren.

Dubban ɗaruruwan al'ummar Annabi daga sassa daban-daban na faɗin ƙasar nan ne suka samu halartar ɗaurin auren, domin taya ango da amarya murna da Allah sanya alheri.

                 Ango da tawagarsa. 

Muna godiya ga Allah, tare da fatan Allah ya sanya albarka a rayuwar auren, ya ba su zaman lafiya da zuriya nagartacciya.

-Muhammad Yankara
 madadin abokan ango
210122

No comments