Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ƙalubalanci jami'an zaɓe na hukumar da ke ofishin ta na Gun...
Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ƙalubalanci jami'an zaɓe na hukumar da ke ofishin ta na Gundumar Babban Birnin Tarayya da su tabbatar da cewa an cimma nasara a zaɓuɓɓukan da za a yi na ƙananan hukumomin yankin a ranar 12 ga Fabrairu.
Farfesa Yakubu ya faɗi haka ne a lokacin da ya kai ziyara ga jami'an zaɓe da sauran ma'aikatan INEC da ke ofishin hukumar na gundumar a garin Abuja a ranar Laraba inda su ka tattauna kan zaɓen da za a yi.
Yakubu ya ce ofishin INEC na yankin Abuja bai da wani uziri da zai iya ba 'yan Nijeriya idan ya gaza cimma nasara, domin kuwa hedikwatar hukumar ta yi dukkan abin da ya kamata ta yi wa ofishin ta na gundumar domin gudanar da wannan zaɓe.
Ya bayyana fatan alherin cewa da yake akwai ƙwararrun jami'an zaɓe a ofishin INEC na gundumar waɗanda sun gudanar da zaɓuɓɓuka a baya, ba su da wani uziri da za su bayar a kan gudanar da wannan zaɓe na ƙananan hukumomin.
Ya ce, “Mun shata layin inganci wajen gudanar da karɓaɓɓen zaɓe a Nijeriya, don haka zaɓen gundumar Abuja ba zai kasa a hakan ba.
“Ko ma menene, za ku ga an samu ƙarin inganci wajen shirya karɓaɓɓen zaɓe a gundumar Babban Birnin Tarayya."
Yakubu ya ce kamar yadda aka aiwatar da zaɓuɓɓuka kwanan baya a jihohin Anambra da Delta, hukumar INEC za ta yi amfani da na'ura mai suna 'Bimodal Voter Accreditation System' (BVAS) a zaɓen Abujan.
Ya ce, “Za mu sake tsara na'urar don ta yi daidai da kowace rumfar zaɓen Abuja daga yanzu zuwa ranar Juma'a.
“Mu na da isassun ma'aikata, kuma mun horas da su. Mu na da isassun masu tallafawa ta ɓangaren kayan aiki a Cibiyoyin Rajista waɗanda za su garzaya su kai ɗauki don gyara duk wata matsalar na'ura da aka samu a ranar zaɓen.
“Mun gama duk wani shiri na sufuri saboda su samu damar yin zirga-zirga a ranar zaɓe ko da ana buƙatar su je wajen zaɓe.
“Kamar yadda mu ka yi a zaɓuɓɓukan baya, za mu riƙa wallafa sakamakon zaɓuɓɓukan ƙananan hukumomin kai-tsaye ta hanyar intanet daga rumfunan zaɓen, sannan za mu bayyana wanda ya ci zaɓe ba kawai na ciyamomin ƙananan hukumomin ba har ma na kansiloli."
Ya ƙara da cewa an tsara kayan aikin zaɓe masu haɗari bisa yawan jam'iyyun da za su shiga zaɓen.
Har wa yau, shugaban hukumar ya ce akwai 'yan takara 475 a zaɓen waɗanda jam'iyyu 17 da ke takarar su ka zaɓa domin neman muƙamai 68.
Tun da farko a nasa jawabin, Kwamishinan Zaɓe na INEC (REC) na yankin, Alhaji Yahaya Bello, ya yaba wa Shugaban kan saurin da aka yi wajen sakin kuɗin da ake buƙata don gudanar da zaɓuɓɓukan ƙananan hukumomin.
Bello ya bayyana cewa ya zuwa ranar 24 ga Janairu, jimillar katinan masu zaɓe na dindindin (PVC) da aka karɓa a gundumar su ne 103,68 yayin da ba a karɓi guda 265,868 ba.
Ya ce a halin yanzu ana ci gaba da karɓar katinan zaɓen a dukkan ofisoshin INEC na Ƙananan Hukumomi shida da kuma hedikwatar hukumar da ke Area 10, sannan ya ƙara da cewa za a dakatar da karɓar a ranar 4 ga Fabrairu.
Kwamishin zaɓen ya bayyana cewa jimillar masu zaɓe da su ka yi rajista a gundumar Abuja Abuja ya kai mutum 1,373,492.
Bello ya ce a cikin shirye-shiryen da ake yi na zaɓen, hukumar ta fara horas da jami'an kula da zaɓe, wato 'Supervisory Presiding Officers' (SPOs), da jami'an tsaro da sauran su.
Ya ƙara da cewa a cikin Disamba 2021 hukumar ta buɗe gidan yana domin ɗaukar ma'aikatan wucin-gadi, wanda aka rufe a ranar 6 ga Janairu, ya na mai ƙarawa da cewa, “Mun ciro takardun neman aiki a ciki, na sassa daban-daban inda ake buƙatar ma'aikatan, kuma yanzu mu na duba su.
“Daga lokacin da aka buɗe gidan yanar a ranar 6 ga Disamba, mun riƙa ciro takardun neman aiki daga masu neman aiki na muƙaman jami'an duba zaɓe (SPOs), 'Presiding Officer' (PO) da 'Assistant Presiding Officer' (APO).
"Bayan an rufe gidan yanar a ranar 7 ga Janairu, mun samu nasarar ciro jimillar waɗanda mu ke buƙata na muƙamin SPOs, wato 285 daga cikin 638 da su ka nema.
"A shiryen-shiryen da ake yi na zaɓen ƙananan hukumomin na yankin Abuja, an rarraba kuɗaɗe na matakai daban-daban ga jami'an zaɓe domin ɗauko hayar motoci, yi wa janaretoci sabis da zuba masu mai, da sauran su."
Ya ce ya zuwa ranar 25 ga Janairu, an kai sama da kashi 75 cikin ɗari na kayan aikin zaɓe marasa haɗari zuwa ƙananan hukumomin, yayin da ake ci gaba da ilmantar da masu zaɓe gadan-gadan.
Bello ya ce daga yanzu hukumar za ta maida hankali da ƙarfin ta wajen tabbatar da an yi ingantancen zaɓen na watan Fabrairu, mai adalci kuma karɓaɓɓe.
Daga bisani, Shugaban na INEC, Farfesa Yakubu, ya shiga taron sirri tare da jami'an hukumar na ofishin gundumar Abuja don ƙara tattaunawa kan shirye-shiryen da ake yi.
No comments