Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Barcelona Na Son Rabuwa Da Dembele A Janairu Don Samun Ribar Cinikinsa

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta ce dole ne dan wasanta Ousmane Dembele ya bar kungiyar cikin watan nan, matakin da ke zuwa...



Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta ce dole ne dan wasanta Ousmane Dembele ya bar kungiyar cikin watan nan, matakin da ke zuwa bayan gaza cimma daidaito da ya fusata bangarorin biyu.

Dembele wanda kwantiraginsa zai kare a karshen wannan kaka ya sake yin watsi da tayin Barcelona na tsawaita kwantiragi.

A 2017 ne Barcelona ta sayo Dembele daga Borussia Dortmund kan yuro miliyan 135 amma kuma zai rabu da kungiyar ba tare da ta samu ko kwabo daga cinikinsa ba idan har ya ci gaba da zama zuwa karewar kwantiraginsa a karshen wannan kaka.

Daraktan wasanni na Barcelona Mateu Alemany ya ce take-taken dan wasan ya nuna musu bashi da ra’ayin ci gaba da taka leda a kungiyar don haka zai fi dacewa ya tafi a watan da muke ciki na Janairu.

Tun kafin yanzu dai mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Xavi Henandez ya gargadi dan wasan kan kodai ya amince da sabunta kwantiragi ko kuma bar kungiyar kafin karewar kwantiraginsa.

No comments