Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Bayan Zuwan Coutinho Aston Villa Na Harin Digne Na Everton

Kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa ta sanar da kai wa wani mataki a tattaunawar cinikin mai tsaron baya na Everton Lucas Digne...Kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa ta sanar da kai wa wani mataki a tattaunawar cinikin mai tsaron baya na Everton Lucas Digne da aka bayyana farashinsa a yuro miliyan 25.

A wani batu na daban kuma tsakanin kungiyoyin biyu, akwai cinikin Anwar El Ghazi ko da ya ke ba a kai ga bayyana farashin dan wasan na gaba ba, wanda tun bayan zuwan Steven Gerarld Villa ke amfani da shi a matsayin sauyi.

Aston Villa ta fara zawarcin Lucas mai shekaru 28 ne tun bayan da manajan Everton Rafael Benitez ya tsagaita amfani da shi a sahun ‘yan wasan kungiyar ajin farko.

Baya ga Lucas, Villa ta kuma kammala kulla yarjejeniyar karbar aron Philippe Coutinho daga Barcelona karkashin wani kwantiragi da ya sahale iya sayen dan wsan mai shekaru 29 kan yuro miliyan 33 a karshen kaka.

Coutinho dan Brazil ko da shekarar guda da ya share a Bayern Munich matsayin aro akwai makamanciyar yarjejeniyar da ta sahale iya sayensa amma kuma kungiyoyin biyu suka gaza cimma jituwa.

Tuni Coutinho ya kammala gwaje-gwajen lafiya da Aston Villa tun a jiya talata.

No comments