Babbar jam'iyar adawa ta PDP a Nijeriya ta ce Shugaba Muhammadu Buhari bai cika alkawari ko daya da ya daukar wa 'yan ka...
Babbar jam'iyar adawa ta PDP a Nijeriya ta ce Shugaba Muhammadu Buhari bai cika alkawari ko daya da ya daukar wa 'yan kasar ba.
Wannan na zuwa bayan da Shugaban ya yi hira da gidan talabijin na Channels, inda ya bayyana 'yan jam'iyar adawar a matsayin wadanda suka kasa.
Hakan ne ya sa PDP ta mayar da martani ta bakin mataimakin jami'in hulda da jama'a na jam'iyar Ibrahim Abdullahi, wanda ya ce a jerin alkawuran da Shugaba Buhari ya dauka daga 2015 zuwa yanzu babu wanda ya cika.
Ya yi ikirarin cewa daga batun tsaro har zuwa na tattalin arziki ba su ga inda shugaban da jam'iyarsa suka yi wata nasara da ta wuce abin da gwamnatin PDP da ta shude ta yi ba.
A cewarsa shugaban ya ce "za a farfado da tattalin arzikin Najeriya, za a habaka harkar tsaro a kasa, sannan za a yaki cin hanci da rashawa kuma babu inda ka samu kashi daya na nasara a ciki."
Kan batun cewa 'ya'yan jam'iyar sun kasa kamar yadda a ka ambato Shugaban ya fada a hira da Channels, Ibrahim Abdullahi ya ce akwai manyan ministocinsa da a jam'iyar PDP ya dauko su, inda ya bayar da misali da karamin ministan man fetur da kuma na ma'aikatar kula da Niger Delta.
Bugu da kari ya ce yanzu haka jam'iyar APC ta Shugaba Buhari na nan na rokon tsohon Shugaba Goodluck Ebele Jonathan da ta kayar da ya zo ya yi mata takara a 2023.
"Mutanen nan su gama duk wannan bankaura ta su shekara bakwai, su dawo su ce ba su da wani madugu da za su tayar ya gaji Buhari sai sun zo suna neman Goodluck Jonathan da rana ya dawo ya yi takara a jam'iyarsu."
A wani bangare kuma na hirar Shugaba Muhammadu Buhari ya ce bai damu da wanda zai gaje shi a 2023 ba.
"Ban damu da wanda zai gaje ni ba, rabu da shi ya zo ko ma wane ne," in ji shi.
Da yake amsa tambaya kan ko me ke zuwa masa a rai idan ya ji an ambaci zaɓen 2023, Buhari ya amsa da cewa: "Ba matsalata ba ce."
Da aka tambaye shi: "Ba ka damu game da wanda zai gaje ka ba? Sai ya ce: "Bar shi ya zo ko ma wane ne. Na tabbata na ajiye rahoton duk wani abu mai muhimmanci. Bai kamata wani ya kira ni ba da shaida a gaban kotu ba a kan wani abu, idan ba haka ba kuma zai shiga matsala."
Buhari ya ce duk da cewa ba shi da wani É—an takara da yake goyon baya a jam'iyyarsu ta APC mai mulki ya gaje shi amma idan ya bayyana shi za a iya halaka shi.
"A'a, saboda idan na faÉ—a za a iya kawar da shi. Gara na bar shi a sirrance," a cewarsa.
Kamar yadda mai magana da yawun jam'iyyar hamayya ta PDP ya bayyana, a baya an yi ta yada jita-jitar cewa wasu jiga-jigan jam'iyar APC mai mulkin na zawarcin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan na ya dawo jam'iyar don ya tsaya musu takara, wanda hakan ke nuna cewa akwai yiwuwar su fitar da wanda zai wa jam'iyar takara daga kudancin kasar.
-Rahoton BBC
No comments