Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya janye haramcin da ya saka wa Twitter a ƙasar. Kakakin shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya tab...
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya janye haramcin da ya saka wa Twitter a ƙasar.
Kakakin shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya tabbatar wa BBC da hakan.
Ana sa ran daga 13 ga watan Janairun 2022 matakin na gwamnatin ƙasar zai soma aiki.
Tun a watan Yunin 2021 ne gwamnatin Nijeriya ta haramta amfani da Twitter a ƙasar bayan ta yi zargin cewa ana amfani da shafin wajen kokarin tarwatsa kasar ta hanyar yada labaran karya da ke iya haddasa ''tashe-tashen hankula''.
Hakan ya haifar da martani mai zafi daga 'yan Nijeriya da dama da suke kallon matakin a matsayin taka hakkin bil'adama, amma kuma gwamnati ba ta nuna wata damuwa ba, inda ta bar shafin na Twitter a kasar ya ci gaba da kasancewa a toshe.
No comments