Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

'Da Idanuna Na Ga 'Yar Gudun Hijra Na Cin Dusa A Zamfara Don Ta Rayu'

BBC ta labarto cewa kungiyoyin ba da agaji a Nijeriya sun ce rashin kulawar hukumomi ta jefa 'yan gudun hijira da dama cikin...


BBC ta labarto cewa kungiyoyin ba da agaji a Nijeriya sun ce rashin kulawar hukumomi ta jefa 'yan gudun hijira da dama cikin mummunar rayuwa

Hajiya Maryam Aminu ta kungiyar Asshifa'a mai aikin ba da agaji ta fuskar lafiya ta ce da idanunta ta ga wata 'yar guun hijira 'tana cin dusa domin babu abincin da za ta ci ta rayu'.

Ta kara da cewa a kwai matar da ta hadu da ita yayin da suke yin aikin agaji tana aikin surfe suna shan ruwan surfen ita da yaranta saboda ba su da wani zabi.

Ta gamu da yara masu yawa da ba sa samun kulawar kowa wadanda kuma suke fama da munanan rashin lafiya a inda suke zaune.

Wadannan labaruka marasa dadi na faruwa ne a inda yan gudun hijira ke zaune a unguwar Samu Naka da ke Jihar Zamfara.

Ko da yake wakilin BBC ya ce mutanen ba a sansanin 'yan guydun hijira suke ba ko aka killace su, suna zaune ne a gine-gine da mutane suka fara ba a kammala ba.

No comments