Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Daga Yanzu Babu Karatu A Makarantu A Ranar Juma'a A Kaduna -Kwamishinar Ilimi

      Kwamishinar Ilimi ta Kaduna, Halima Lawal  Gwamnatin jihar Kaduna ta umurci dukkanin makarantun Gwamnati a fadin jihar Kad...

      Kwamishinar Ilimi ta Kaduna, Halima Lawal 

Gwamnatin jihar Kaduna ta umurci dukkanin makarantun Gwamnati a fadin jihar Kaduna da su koma bin sabon tsarin aiki na kwana hudu wato Litinin zuwa Alhamis.

MADOGARA ta labarto cewa Kwamishinar ilimi ta jihar Kaduna, Halima Lawal, ita ce ta bayar da sanarwar ga makarantun jihar a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce a yayin da za a soma zangon karatu na Biyu daga ranar Litinin 10 ga watan Janairu, ranar Juma'a ba ta daga cikin ranekun karatu. 

Halima Lawal, ta kara da jan kunnen makarantu da su kiyaye dokokin tsaro da na kiwon lafiya da aka tsara domin kare dalibai. Sannan ta bayar da lambar waya da za a kira a duk lokacin da ake zargin wani abu da ya shafi tsaro a makarantu ko harabar makarantu a jihar Kaduna. 

No comments