Kafafen watsa labarai sun labarto yadda wani Dattijo ya cire rufin gidansa domin ya sayar da kwanon ya biya wa dansa kuɗin fansa...
Kafafen watsa labarai sun labarto yadda wani Dattijo ya cire rufin gidansa domin ya sayar da kwanon ya biya wa dansa kuɗin fansa.
Wani Dattijo mai suna Malam Sa'idu da ke a garin Faskari a yayin da yake ƙoƙarin cire kwanon gidansa ya sayar domin biyan N100, 000 kuɗin fansar ɗansa da aka yi garkuwa da shi.
Rahotanni sun ruwaito cewa, tsohon da bai da cin yau, ballantana na gobe, 'yan bindiga sun yi garkuwa da shi a garin Faskari, 'ya'yansa matasa suka haɗa kuɗin fansa suka kai naira dubu N50, 000, amma sai suka saki tsohon suka riƙe yaron na sa, daga bisani suka nemi karin naira N100, 000 kuɗin fansar yaron.
No comments