Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya ce dole a hukunta tsohon shugaban Amurka Donald Trump bisa kisan babban Janar din sojin kasar Qassem ...
Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya
ce dole a hukunta tsohon shugaban Amurka Donald Trump bisa kisan babban Janar din
sojin kasar Qassem Soleimani shekaru biyu da suka wuce, idan ba haka Iran za ta
yi ramuwar gayya.
A wani jawabi da ya gabatar ta gidan
talbijin ranar Litinin, shugaban kasar ta Iran ya ce “babban mai laifi kuma
makashi” wanda ya bayar da umarnin kai hari da jirgi maras matuki a kan jerin
gwanon motocin Soleimani a Iraki, Trump dole ne ya fuskanci “shari'ar Allah”
sannan ya fuskanci “qisas”, wanda a Musulunce yake nufin ramuwar gayya.
Raisi ya yi kira a kafa “kotun
adalci” wadda Trump, da tsohon Sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo da
sauran jami'an kasar za su gurfana a gabanta sannan a hukunta su.
No comments