Daga Muhammad Farouk Idan Allah ya kaimu gobe Juma'a 21 ga watan Janairun 2022, za a daura auren Babban Editanmu Ammar Muham...
Daga Muhammad Farouk
Idan Allah ya kaimu gobe Juma'a 21 ga watan Janairun 2022, za a daura auren Babban Editanmu Ammar Muhammad Rajab.
Ammar Muhammad Rajab shi ne Babban Editan shafin www.madogara.com.ng. Kuma shi ke kula da shafinmu na Madogara TV/Radio dake Facebook da kuma Madogara Radio dake Manhajar ZenoFm.
Za a daura aurensa ne da zankadediyar Amaryarsa Maimuna Nasiru Aliyu Na'Allah Zurmi da misalin karfe 1:30 a Masallacin Shaikh Lawal Abubakar dake Gada Biyu a Garin Gusau ta jihar Zamfara.
Kazalika a washegarin wannan rana wato ranar Asabar, 22 ga watan Janairun 2022 za a gabatar da gagarumin walimar auren a Queens Land Park dake No 1 ÆŠorawa Road G R A Zariya ta jihar Kaduna.
Za a yi walimar ne da misalin karfe 3 na yammacin wannan rana.
No comments