FARGABA: Duk Wanda Zai Shiga Fadar Buhari Sai An Masa Gwajin Korona

 


Daga yanzu masu kai ziyara Fadar Shugaban NIjeriya sai sun yi rigakafin korona kafin a ba su damar shiga fadar mulkin ta Aso Rock Villa da ke Abuja.

A cewar mai magana da yawun shugaban ƙasa, Garba Shehu, wajibi ne a yi wa duk mai ziyara gwajin a kyauta a bakin ƙofa.

Cikin waɗanda dokar ta shafa har da gwamnoni da sauran manyan ƙasa sannan kuma ba waɗanda za su ga shugaban ƙasa ba kawai.

Sai dai ya ce akwai wasu shugabannin ƙasar waje ba lallai sai an yi musu ba "duk da cewa su ma ana ba su shawarar su yi gwajin".

"Kyauta ake yin gwajin saboda haka babu wanda zai biya ko ƙwandala...duk wani mai ziyara, ba masu ganin shugaban ƙasa kaɗai ba, dole ne ya yi gwajin gaggawa a bakin ƙofa."

Post a Comment

0 Comments