Daga Wakilinmu A ci gaba da bayar da tallfi ga 'yan gudun hijira tuni dai wannan gidauniyar ta raba kaya da dama ga 'ya...
Daga Wakilinmu
A ci gaba da bayar da tallfi ga 'yan gudun hijira tuni dai wannan gidauniyar ta raba kaya da dama ga 'yan gudun hijirar dake zaune a Firamare dake Anka jihar Zamfara.
Abubuwan da aka rabawa wadanda suka amfana da tallafin sun hada da buhunan shinkafa, kayan sawa ga mata da yara.
Lokacin da ya ke jawabi a yayin raba kayan tallafin wanda aka yi a harabar makarantar da ke Anka, shugaban kungiyar, Mu'azu Yusuf Dangaladima, ya bayyana cewa wannan karimcin wani bangare ne na ayyukan agaji ko taimako da kungiyar ke yi ga wadanda rikicin 'yan bindiga da sauran bala'o'i suka shafa a jihar wadanda suke zaune a cikin garin Anka.
Kamar yadda Mu'azu Dangaladima ya bayyana, kungiyar ta samar da taimako ko agaji makamancin hakan ga 'yan gudun hijira a sansanoninsu.
"Mun yanke shawarar mu zo mu taya ku jimamin abin da ya faru 'yan kwanakin nan inda 'yan bindiga suka kashe mutane da yawa, kuma da yawa suka rasa muhallansu."
"Kamar yadda ya ke a al'adar wannan kungiya, mun yanke hukuncin mu rage maku wahalhalun da mafi yawancinku za su iya fuskanta a lokaci mai tsawo." Kamar yadda shugaban kungiyar ya bayyana.
Shugaban kungiyar har wa yau ya mika jajen kungiyarsa ga wadanda wannan ibtila'i na rashin imani wanda 'yan bindiga ke nunawa ya shafa su da iyalansu.
Ya yi addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu ya kuma kawo dawwamammen zaman lafiya a jihar da Nijeriya baki daya.
A cikin jawabinsa jim kadan bayan rarraba kayan, shugaban kwamitin da ke kula da 'yan gudun hijira a masarautar ta Anka, Alhaji Aliyu Dan Akalele wanda mataimakinsa, Alhaji Abdulmumin Anka (Chiroman Anka) ya wakilta, ya bayyana jin dadinsa akan wannan agaji da aka kawo, sai kuma ya yi addu'ar Allah Ya saka wa kungiyar da alkhairi.
"Zan iya tunawa da kyau lokacin da kuka rarraba irin wadannan kaya ga 'yan gudun hijira a wannan masarauta, yau ma kuma kun kara yin wannan karamci, muna matukar godiya a gareku." Chiroman ya bayyana
Kwamitin da ke kula da 'yan gudun hijira na masarautar ne ya kula da rarraba kayan ga 'yan gudun hijirar da kuma wasu na hannun daman tsohon gwamnan jihar, Abdul'aziz Yari wadanda suka hada da APC karamar hukumar Anka, mataimakin shugaban Yari Factor, Alhaji Bello Ahmed, Alhaji Bello Alinko Anko da kuma Alhaji Bello Ahmed Rafin Gero da sauran 'yan jam'iyya da ke karamar hukumar.
An yi taro lafiya an tashi lafiya.
No comments