Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Gobara Ta Lakume Dukiyar Naira Tiriliyan Uku A Nijeriya'

Gobara ta lalata dukiyar da ta kai ta naira biliyan dubu 3, wato tiriliyan 3 a Najeriya, kamar yadda Ministan harkokijn cikin gi...


Gobara ta lalata dukiyar da ta kai ta naira biliyan dubu 3, wato tiriliyan 3 a Najeriya, kamar yadda Ministan harkokijn cikin gida na kasar, Rauf Aregbesola ya bayyana.

Ministan ya ce kasar ta tafka wannan asara ne a sanadiyyar gobara 2,845 da aka samu a sassan kasar daban-daban a shekarar da ta wuce, 2021.

Aregbesola ya sanar da haka ne jiya Laraba yayin da yake sanya lambobin karin girma ga manyan shugabannin hukumar kashe gobara ta tarayyar kasar, a Abuja.

Ministan ya kuma ce hukumar ‘yan kwana-kwana ta yi nasarar kare kadarar da ta kai ta naira tiriliyan 18.9 trillion da ceto mutane 260 daga gobara.

Ministan, wanda ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa tare da kai dauki na kashe gobara har 2,845 a shekarar da ta wuce 2021, y ace sun samu wannan nasara ne saboda a tsakanin 2015 zuwa yanzu hukumar ta samu kayan aiki fiye da yadda take samu tun lokacin da aka kirkiro ta a 1991 kamar yadda rahoton BBC ya tabbatar. 

1 comment

  1. Youtube
    youtube.tv › tvl-videos › youtube_tvl › tvl-videos › youtube_tvl youtube to mp4 youtube.tvl youtube.tvl youtube.tvl youtube.tvl youtube.tvl youtube.tvl youtube.tvl youtube.tvl youtube.tvl youtube.tvl youtube.tvl youtube.tvl youtube.tvl youtube.tvl youtube.tvl youtube.

    ReplyDelete