Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Hadakar Kungiyoyin Fararen Hula Na Arewa Maso Yamma Sun Gudanar Da Zaben Nuna Goyon Bayansu Ga Dakta Mustapha

Daga Wakilinmu Hadaddiyar kungiyar ta yi taron ne don nuna goyan baya ga shugabanni masu himma ciki har da Darakta a cibiyar kul...Daga Wakilinmu

Hadaddiyar kungiyar ta yi taron ne don nuna goyan baya ga shugabanni masu himma ciki har da Darakta a cibiyar kula da kunne ta kasa da ke Kaduna, inda suka shirya tsaf domin gudanar da taron kasa baki daya. 

Hadakar kungiyoyin fararen hula da suka hada da kungiyoyi sama da 200 sun gudanar da zaben nuna goyon bayansu ga likita kuma Daraktan cibiyar kula da kunne ta kasa sakamakon cigaba da aka samu a cikin shekaru uku da ya yi a ofis. Wannan ne kuma ya sa ya ke samun yabo. 

Kungiyar wadda ta hadu a yau 19 ga watan Janairu, 2022 a yayin babban taron ta na shekara wanda aka yi a Abuja domin tattauna cigaban da aka samu a cikin kasafin kudin shekarar 2021 wanda aka yi duba gareshi bangare - bangare. 

Mai kula da tsare-tsare na kasa, Comrade Abdullahi Abdulrauf ya ce, "Muna matukar sa ido ga bangaren kiwon lafiya domin kuwa wani bangare ne da ya shafi rayuwar kowanne dan Nijeriya kuma muna alfahari da cewa shugabancin Dakta Mustapha Abubakar Yero shine aka yi hashashen wanda ya fi kowanne kyau ta fuskar mulki, samar da bayanai, cigaban mutane da kuma jarinsu."

A lokacin da aka tambayesa ko da me ya yi amfani wajen wannan awo, sai ya ce an samar da wani kwamiti domin ya ziyarci dukkanin cibiyoyin lafiya na tarayya, ayyukan da aka gani an ga ko dai an kammala ko ana kan yi, an rarraba takardun tambayoyi ga ma'aikata da marasa lafiya a yayin wannan aikin kuma muna alfahari da cewa ya samu maki 98% inda cibiyar da ke bi ma wannan ta samu 60%.  Wannan nasarar ba za ta fadi kasa banza ba. 

Comrade Abdullahi ya bayyana cewa a cikin 'yan satuka, za mu shirya taron kasa baki daya domin mu nuna yabo ga kokarin Dakta Mustapha kuma mu fadawa duniya cigaba da dama da aka samu. 

Kadan daga cikin wasu cigaban da aka samu sun hada da cigaban bangaren kayayyakin lafiya, ayyukan yi ga kusan ma'aikatan lafiya  100 a kowanne fanni, horo ga ma'aikata a cikin gida da wajen Nijeriya domin tabbatar da samar da kyakkyawan aiki, dakin bincike-bincike mai na'u'rori, daga darajar sashen tiyata wanda wadannan kadan kenan kamar yadda mai kula da tsare-tsaren na kasa ya bayyana. 

Sun ma yi jinjina ga ministan lafiya domin irin taimakon da ya ke yiwa asibitin wanda hakan ya sa aikin Dakta Mustapha ya ke tafiya da kyau. 

Sai daga karshe ya yi kira ga daraktan da ya cigaba da ayyukan alkhairi da ya ke yi wadanda suka yi daidai da gyare-gyare da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke yi.

No comments