Al'umma da gwamnatin jihar Neja sun bayyana kyakkyawan fata a kan gagarumin aikin sojin da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar...
Al'umma da gwamnatin jihar Neja sun bayyana kyakkyawan fata a kan gagarumin aikin sojin da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da ƙaddamarwa a shekaran jiya Lahadi da nufin raba jihar da 'yan fashin daji da kuma sauran 'yan Boko Haram.
Wasu mazauna jihar sun shaida wa BBC cewa ko da yake, har yanzu ba su fara ganin ko alama ta wannan aikin soji na musamman ba, amma dai mataki ne da ya zo a lokacin da suke tsananin buƙata.
Sun ce Mashegu na cikin yankunan da a yanzu suka fi É—andana kuÉ—arsu a hannun 'yan fashin daji.
Ɗumbin mutane sun baro ƙauyuka inda suka zo suka tare suna zaman gudun hijira a garuruwan da suka fi aminci da rayuwa cikin mawuyacin hali.
Wata majiyar tsaro a yankin ta shaidawa BBC ko a jiya Litinin an fafata tsakanin jami'an tsaro a yankin Gana, a ƙoƙarin bin sawun 'yan fashin da ake jin sun kora shanun da ake ƙiyastawa sun kai dubu daga Mashegu a harin ranar Asabar.
Haka zalika, a baya-bayan nan dai an sace fiye da mutum 40 a yankin Nkwai, sai kuma ƙarin mutum a Unguwar Bakanike.
A makon jiya ma, an yi wa manoma kimanin talatin kisan gilla a ƙauyukan Wurukuci da Nakudna a ƙaramar hukumar Shiroro.
Wani shaida ya ce garuruwan Mariga da Durgu da Kwanar Mariga da Kamfanin Bobi sun cika maƙil da mutanen da suka tsere wa ƙauyukansu saboda yawan hare-haren 'yan fashin daji
Zuwa yanzu dai duk mutanen da na zanta da su daga Mariga da Mashegu sun ce ba su fara ganin gagarumin matakin soji da Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar ranar Lahadi ba.
Gwamnatin jihar Neja dai ta bakin Sakataren Gwamnatin Jihar Ahmed Ibrahim Matane ta ce babban aikin sojojin, wani babban abin maraba ne.
Ahmed Matane ya ce ban da yankunan da 'yan fashin daji suka addaba, akwai kuma yankin ƙaramar hukumar Borgu inda gyauron 'yan Boko Haram tsagin ISWAP suka yi wa kaka-gida
Sakataren Gwamnatin jihar Neja dai ya ce yanzu haka shi da kansa ba zai iya zuwa ƙauyensu Matane a ƙaramar hukumar Mashegu cikin daɗin rai ba.
Ya ce babban burinsa shi ne a wayi gari a jihar Neja, ba tare da an samu rahoton kai wa wani ƙauye hari ba, abin da ya ce zai ƙarfafa gwiwar masu sha'awar zuba jari zuwa Neja, don su taimaka wajen farfaɗowa da haɓaka tattalin arziƙinta.
-Rahoton BBC
No comments