Al'umomin jihar Borno sun ce har ya zuwa yanzu babu labarin dalibai mata 110 daga cikin 276 da mayakan boko haram suka sace ...
Al'umomin jihar Borno sun ce har ya zuwa yanzu babu labarin dalibai mata 110 daga cikin 276 da mayakan boko haram suka sace a Sakandaren Chibok a shekarar 2014 kamar yadda Rfi ta labarto.
Wata kungiyar da ake kira Kibaku ta raya Yankin Chibok, wadda ke sahun gaba wajen fafutukar ganin an ceto 'yan matan ta hannun shugaban ta Dauda Iliya ya ce daga cikin daliban 276, 57 sun yi nasarar gudu daga hannun wadanda aka yi garkuwa da su.
Iliya ya ce daga shekarar 2012 zuwa yanzu an kashe mutane sama da 72 a yankin, yayin da aka sace sama da 407, tare da kona gidaje da wuraren sana’oi da mujami’u da kayan abinci da kuma sace motoci sama da 20.
Shugaban al’ummar ya ce daga karshen shekarar 2018 zuwa yanzu, mayakan Boko Haram sun zafafa hare-haren su a yankin, ciki harda wanda aka kai Kautikari a ranar 14 ga wannan wata inda aka sace 'yan mata 5 tare da kashe mutane 3 da kuma kona gidaje da mujami’u.
Jami’in ya ce har yanzu suna jiran hukumomin Nijeriya su ceto musu dalibai mata 110 da aka sace a shekarar 2014, tare da bukatar kara yawan sojoji da kayan aiki a Chibok domin dakile hare-haren da ake kai musu.
No comments