Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Himma Bata Ga Rago Initiative Ta Gudanar Da Babban Taron Shekara Karo Na Biyu

Abubakar M Tahir Himma Bata Ga Rago Initiative ta gudanar da babban taron ta na shekara karo na biyu a garin Hadejia. Kungiyar d...


Abubakar M Tahir

Himma Bata Ga Rago Initiative ta gudanar da babban taron ta na shekara karo na biyu a garin Hadejia.

Kungiyar da ta Ƙunshi Malaman Jami'o'i, Kwalejin ilimomi, masana, kwararru, ma'aikatan asibiti ƴan asalin masarautar Hadejia.

A bana sun shirya taron ne kan matsalar da take cima al'umma tuwo a kwarya. Taken taron na bana a Turance shi ne "Sustainable Financing Community Development Project". Wanda yake magana kan hanyoyi masu inganci da za a dauki nauyin ci gaban al'umma.

Taron na bana ya samu halartar kungiyoyi goma sha takwas wanda suka fito daga sassa daban-daban na masautar Hadejia.

Wanda suka gabatar da kasidu sun haÉ—a da Dr. Ibrahim Rakakaya Darakta a 'Jigawa State Rehibilitation Board', Sai Kwamishinan Gidaje da Safiyo Honorabul Sagir Musa da kuma Sakatare kasafi da tsare-tsare Malam Abbas.

Taron ya samu halartar manyan bakin  Ciyamomin karamar hukumar Hadejia da Malam Madori, Honorabul Abdulkadir Bala T.O da Honorabul Hussaini BK sai wakilin dan majalisar wakilai mai wakiltar Malam Madori/ Kaugama Honorbul Makki Abubakar Elleman.

A karshe aka karrama kungiyoyi ci gaba garin da wanda suke bada kokari wajen ci gaban kungiyar da Satikifen na girmamawa.

Da yake zantawa da manema labarai Shugaban Kungiyar Dr. Mustapha Hussaini Garun Gabas daga Jam'iar Sule Lamido dake Kafin Hausa ya kawo dalilin bude kungiyar.

Dr. Garun Gabas ya kara da cewa; "mu Allah ya mana baiwar ilimi mai zurfi wanda muke gudanar da bincike, muna so mu yi amfani da ilimin mu wajen magance matsalar dake damun al'ummar mu", inji shi. 

Dr. Hussaini Garun Gabas ya karkare da kira ga Æ´an'uwansa matasa kan tashi tsaye wajen neman ilimi domin zamantowa ababe! alfahari cikin al'umma.

No comments